Taskar Arewa

Barka da zuwa shafin Taskar Arewa shafin dake yada al'adun hausawa dakuma abubuwan dasuka shafi Hausawa

Matashi A Kano Ya Hada Mota Mai Amfani Da Hasken Rana

Wallafan watanni 4 da suka wuce. Na Yahaya Bala. A Sashin Kirkire Kirkire

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/08/1165/_92304316_20161102_021823_resized.jpg
Wani matashi a birnin Kano na arewacin
Najeriya ya kirkiri wata mota mai amfani da
makamashin hasken rana a maimakon man fetur. Matashin, Mukhtar Adamu Fasaha, dan shekara 23 ya ce motar, wadda ta yi tafiyar sama da kilomita 1 a wani gwaji da ya yi, an hada ta ne da karafa da katakai da batur da faifan zuko
hasken rana. Ya ce faifan, wanda ya yi wa motar rumfa, shine yake bai wa batirin motar wuta. Tana kuma amfani da wani moto irin na injin jawo ruwa wanda yake samun wuta daga batirinta, sannan ya juya kundun giya, ta yadda
tayoyinta za su fara tafiya.
An sanya wa motar kundun giya da tayoyin babur Vespa, kuma ana iya inganta fasahar wajen rage dogaro da man fetur zuwa amfani da makamashi maras gurbata muhalli, don harkokin sufuri a kasashen Afirka kamar Nijeriya.
A cewar matashin, idan akwai kayan aiki, ana iya inganta ta, a fadada ta, a musanya katakan da ke jikinta da karfe yadda za ta fi karko da jan hankali. Mukhtar ya kuma ce ya shafe kimanin shekara biyu yana tara kayan hada motar, amma a cikin kwana 11 ya hada ta. "Akwai abubuwan da za a iya saukaka ta'ammali da man fetur din kamar irin wadannan (motoci) in aka yi su manya-manya haka. Ka ga an samu sauki ma ke nan", inji shi.
Motar mai fadin inci 40 da tsawon inci 72 tana da mazaunin mutum biyu ne amma matashin ya
ce tana da karfin daukar mutum hudu. Ya ce ya sayi kayayyaki da dama, wasu kuma ya tsince su
don hada wannan mota da ke iya tafiya har ma da baya da baya. An sauya fasalin moto dinta daga ainihin karfin voltage 480 da yake da shi zuwa voltage 360 ko 240 ta yadda batirin da aka sa mata zai iya dadewa yana aiki ba tare da ya ja lantarki mai
yawa ba. Matashin ya ce idan aka sa wa motar ingantaccen batir mai karfi zai iya ba ta wutar da
za ta yi gudu a lokaci guda kuma ta adana wani
bangare na lantarki ko da za a shiga yanayin da ba hasken rana. Ya kuma ce an tsara fasahar motar ce yadda ba za ta dinga fitar da hayaki ko yin wata k'ara ba,
amma saboda ba a goge kacar da aka sanya mata ba, tana yin guga.
Ya zuwa yanzu ba a tantance gudun kilomita nawa take iya yi a cikin sa'a guda ba, amma dai makerin motar ya ce zai yi hakan a nan gaba idan ya sauya mata batir.
Samun Labari Daga BBC Hausa

Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Matashi A Kano Ya Hada Mota Mai Amfani Da Hasken Rana"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Game Da Mai Wallafa

Yahaya Bala, Mai son rubuce-rubuce aharshen Hausa, Shine yakirkiro shafin kuma yake wallafa bayanai awannan shafinna Taskar Arewa


Game Da Mu

Shafin Taskar Arewa na kawo muku abubuwan dasuka shafi hausawa yan arewa da kuma abin dake wakana akasar Hausa.
Manufar mu Shine mu fadakar da kuma yada al'adu a ko'ina, da kuma nishadantar da al'ummah aduk inda bahaushe yake.


Labarai Da Dumi-Duminsu

Zamu kawo muku labaran duniya dadumi-duminsu dakuma labaran fasaha da dai sauransu....


Kasidu Masu Alaka