Taskar Arewa

Barka da zuwa shafin Taskar Arewa shafin dake yada al'adun hausawa dakuma abubuwan dasuka shafi Hausawa

Da ka nake rera dukkan wakokina - Ado gwanja

Wallafan watanni 5 da suka wuce. Na Yahaya Bala. A Sashin Nishadantarwa

Fitaccen mawakin nan na Hausa kuma wanda yake fitowa a fina-finan Kannywood Ado Gwanja ya ce ya rera kusan wakoki 600 tun da ya soma sana'arsa ta waka kuma galibinsu da ka ya rera su.
Ado Gwanjo ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa Instagram Live ranar Alhamis.
Da aka tambaye shi ko yin waka yana da wahala, sai ya ce "gaskiya babu abin da yake ba ni wahala" idan ya zo rera waka.
"Ina kiran mai kida na ce 'buga min kida yanayi kaza, ko yanayi kaza', sai a yi min kida sikeleton...ina cikin ji wakar za ta zo. Idan ta zo sai na ce 'samo min furodusoshi," a cewar Ado Gwanja.
Ado Gwanja ya ce cikin kusan waka dari shida da ya yi, wakoki ba su wuce biyu ba wadanda ya zauna ya rubuta saboda wasu sun ba shi shawarar yin hakan.

BBC Hausa

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/07/1165/gwanja.jpg

Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 2 a kan "Da ka nake rera dukkan wakokina - Ado gwanja"


Babu hoto01-07-2020
Khalil

Gaskiya abun da mamaki


Babu hoto01-07-2020
Khalil

Gaskiya abun da mamaki

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Game Da Mai Wallafa

Yahaya Bala, Mai son rubuce-rubuce aharshen Hausa, Shine yakirkiro shafin kuma yake wallafa bayanai awannan shafinna Taskar Arewa


Game Da Mu

Shafin Taskar Arewa na kawo muku abubuwan dasuka shafi hausawa yan arewa da kuma abin dake wakana akasar Hausa.
Manufar mu Shine mu fadakar da kuma yada al'adu a ko'ina, da kuma nishadantar da al'ummah aduk inda bahaushe yake.


Labarai Da Dumi-Duminsu

Zamu kawo muku labaran duniya dadumi-duminsu dakuma labaran fasaha da dai sauransu....


Kasidu Masu Alaka